Isa ga babban shafi
Faransa

An shirya gangami kan matsalar canjin yanayi a duniya

Dubban mutane sun shirya gangami a wasu manyan biranen duniya da dama a yau lahadi domin yin kira ga shugabannin duniya su gaggauta amincewa da matakin rage gurbataccen iska a taron canjin yanayi da za a soma a birnin Paris a gobe Litinin.

Zanga-zangar canjin yanayi a Adelaide, kudancin Australia
Zanga-zangar canjin yanayi a Adelaide, kudancin Australia REUTERS
Talla

An shiya gangamin ne a biranen Sydney na Australia da Seoul na Koriya ta kudu Rio de Janeiro na Brazil da New York na Amurka da Mexico City da wasu birane da dama.

An gudanar da gangamin a ranar Assabar a kasashen New Zealand da Philippines da Bangladesh da Japan da Afrika ta kudu da Birtaniya UK.

Masana sauyin yanayi sun ce dumamar yanayi ne ke haifar da karancin ruwan sha da kuncin rayuwa da kananan kasashe ke fama da shi musamman kasashen Afrika da gabas ta tsakiya wadanda al’ummarsu yanzu ke ci gaba da kwarara zuwa kasashen Turai.

A gobe ne kuma za a soma taron canjin yanayi a Paris wanda zai kunshi shugabannin kasashen duniya sama da 150 da suka hada da Shugaban Amurka da Rasha da China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.