Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus ta dauki alhakin kisan Yahudawa

Kasar Jamus ta ce ta dauki alhakin kisan gillar da Adolf Hitler ya yiwa Yahudawa bayan Firaminstan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa shugaban Falasdinawa ne ya bai wa Hitler shawarar hallaka su.

Firaiministan Isra'ila Benyamin Netanyahu da shugabar gwamanatin Jamus Angela Merkel.
Firaiministan Isra'ila Benyamin Netanyahu da shugabar gwamanatin Jamus Angela Merkel. AFP PHOTO / JOHANNES EISELE
Talla

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ba su ga dalilin jawabin na Netanyahu ba, wadda ta ce na neman sauya tarihin da aka sani ne.

A ziyarar da ya ke yi a Jamus, Netanyahu ya bayyana cewa Hitler bai da shirin kashe Yahudawa har sai da ya hadu da shugaban Falasdinawa Haj Amin Al Hussein, babban limamin birnin Qudus wanda ya ba shi shawarar hallaka su saboda kar ya ba su damar koma wa birnin Qudus.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.