Cin zarafin Mata na karuwa a Duniya
Wani sabon Rahoton Majalisar Dinkin Duniya na cewa, cikin shekaru 20 da suka gabata, mata sun fi tsawon rai a fadin duniya, kuma ana samun bunkasar ilimi zamani tsakanin su, sai dai wani babban abinda ke addabar su shine yadda ake cin zarafin su da tauye musu hakki.
Wallafawa ranar:
Wannan rahoto na kunshe ne cikin wata kasida da aka kwashe shekaru biyar ana nazari a kai a Sassan kasashe 102 da ke duniya, inda aka gano cewa kashe 1 cikin 3 na mata na fuskantar munanar cin zarafi.
A cewar Jagoran Binciken Francesca Grum, Rahoton wanda shine karo na 6 da Majalisar ta fitar na cewa fasalin cin mutuncin mata da aka binciko, kalilan daga cikin wadan da aka tauyewa hakkin su ne kawai ke iya kare kan su.
Grum wanda ke cewa cin zarafin mata matsalar ce da ke sake ta’azara a duniya, ta ce kashe 70 zuwa 90 na mata cikin 100 suke dawainiya da Iyalansu.
Majalisar Dinkin Duniya dai na cewa sama da rabin kasashe a duniya da mata ke wahala a wajen aiki sama da maza, a kan basu hutun haihuwa sati 14 kaccal wanda kamata ya yi yafi haka.
Sai dai kuma Majalisar ta yaba da ci gaban da ake samu a fanin ilimin mata a duniya tare da kuma bayyana cewa a wannan zamani mata kan yi tsawon rai har zuwa shekaru 72 a duniya sabanin maza da yawanci basa haura shekaru 68.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu