Isa ga babban shafi
Malaysia

An gano bangaren jirgin Malaysia da ya yi batan dabo

Binciken da aka gudanar akan wani katafaren allon  jirgin sama da aka gano a tekun India ya tabbatar da cewa na Jirgin Malaysia ne da ya bata yau watanni 18  dauke da mutane 236.Samun allon jirgin da masana a Faransa ke nazari akai ya kawo karshen fatar iyalan fasinjojin jirgin.

Allon da aka tabbatar da cewa na jirgin Malaysia ne da ya yi batan dabo
Allon da aka tabbatar da cewa na jirgin Malaysia ne da ya yi batan dabo Reuters
Talla

Firiya Ministan Malaysia Najib Razak ne ya tabbatar da cewa na jirgin kasar ne Samfurin MH370 da ya yi hadari yau kwanaki 515, kuma binciken da akayi kan wasu sassan jikin sa da aka samu, ya tabbatar musu da cewar jirgin ya fadi ne.

Tuni dai Najib Razak ya kara jinjinawa iyalan wadanda suka rasa ‘Yan’uwansu a hadarin jirgin.

Sai dai ‘yan’uwan mamatan sun nuna rashin gamsuwarsu inda suka bukaci karin bayani dangane da yadda hadarin ya auku.

Sanarwar Firayi Ministan dai ya kawo karshen zama na zulumi da damuwa da al’ummar kasar dama yan’uwan fasinjojin suka sami kan su tun bayan da jirgin ya yi batan dabo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.