Isa ga babban shafi
Malaysia

A Faransa za a yi binciken tarkacen jirgin da aka tsinta

Wani lokaci a karshen wannan mako, za a iso da wani bangare na tarkacen jirgin sama da aka gano a tsibirin Reunion da ke tekun Indiya a kasar Faransa domin bincike akai.

Ana tunanin tarkacen da aka tsinta a Tekun India na jirgin Malaysia ne Boeing 777 ko MH370 da ya bata
Ana tunanin tarkacen da aka tsinta a Tekun India na jirgin Malaysia ne Boeing 777 ko MH370 da ya bata Photo: Yannick Pitou/AFP
Talla

Masu bincike dai na zaton cewa wani katafaren allon jirgin sama da aka gano a cikin teku, ya yi kama da na jirgin fasinjar Malaysia da ya bata dauke da mutane 239 a shekara ta 2014.

A yau juma’a masu aikin bincike a kasar Australia da kuma Faransa sun ce suna da yakini cewa inda aka gano wannan tarkace, ko shakka babu yana daga cikin yankunan da aka gudanar binciken farko a lokacin da wannan jirgi ya fado a cikin watan Maris na shekarar bara.

Kasar Australia dai ita ce ke jagorantar aikin binciken sanin abin da ya faru da jirgin na kasar Malaysia, wanda ya bata yana dauke da fasinjoji 239 ranar 8 ga watan Maris na shekarar bara, akan hanyarsa ta zuwa birnin Beijing kasar China bayan ya taso daga Kuala Lumpur.

Tun lokacin faruwar lamarin ne ake ci gaba da aikin bincike, amma sai a shekaranjiya Talata ne lokacin da aka gano wani katafaren sashen na jirgin sama da ake zaton cewa shi ne ya bata a shekarar ta bara.

Yanzu dai hankula sun soma karkata ne zuwa ga irin sakamakon da masu bincike za su fitar bayan gabatar da wannan bangare na jirgi da aka gano a wata cikakkiyar cibiyar bincike a kasar Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.