Isa ga babban shafi
Faransa-China

Faransa da China za su bunkasa Afrika da Asiya

Kasashen China da Faransa sun sanar da wani shirin hadin gwuiwa dan aiki tare wajen ayyukan bunkasa kasahsen dake nahiyar Afirka da Asia wanda kowa zai amfana da shi.

Shugaban Kasar China Xi Jinping da Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Kasar China Xi Jinping da Shugaban Faransa Francois Hollande REUTERS
Talla

Firaministan China Li Keqiang ne ya sanar da wannan sabuwar dangantaka ta bazata yayin ziyarar Faransa a ganawar da yayi da takwaransa Manuel Valls.

Yarjejeniyar da suka sanya hannu a kai ta kunshi yin aiki tare wajen gina kayan more rayuwa da kuma samar da wutar lantarki wanda zasu dinga yi tare a tsakanin su.

Li ya ce abinda za su mayar da hankali akai shine samar da masana’antu, rage talauci da kuma gina hanyoyi, samar da ruwan sha da makamantan su.

A baya kasahsen Turai sun zargi China da kutse cikin nahiyar Afirka inda take kwace musu kawayen da suka dade suna aiki tare.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.