Isa ga babban shafi
MDD-Africa

Safarar hodar iblis ya ta’azara-Rahoto

Alkallumar da Majalisar dinkin duniya, ta fitar a yau alhamis na nuni da cewa a cikin watan da ya gabata Jami’an tsaro sunyi nasarar kwace hodar ibilis da nauyinta ya kai ton daya da rabi a gabar ruwan yankin gabashin Afrika.

Hodar Iblis da 'yan sintiri Faransa suka kama
Hodar Iblis da 'yan sintiri Faransa suka kama AFP PHOTO PATRICE COPPEE
Talla

Bayanin Majalisar dai ya ce Jami’an tsaro da ke sintiri a kan tekun India ne suka kama wannan hoda daga hannun manyan dillalai da ke fataucin ta zuwa sauran sassan duniya.

Rahotan ya kuma kara da cewa a cikin watanin Mayu da Yuni da suka gabata, ‘yan sintirin daga kasashen Australia da Britaniya da Faransa da kuma New zealand sun kaddamar da wani aikin haddin guiwa da ya kai su ga kamen hodar iblis da adaddin sa ya kai na dala miliyan 675.

Alkallumar da Majalisar ta ce na nuna karuwar mu’amala da hodar ya ta’azara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.