Isa ga babban shafi
MDD

MDD tace ana samun raguwar yunwa a Duniya

A Rahotan shekara-shekara data fitar a yau laraba, Hukumar abinci ta Majalisar dinkin duniya, ta ce alkallumar mutane da ke fama da matsanancin yunwa ya sauka, kasa da miliyan 800. Karon farko daga lokacin da hukumar ta fara sa ‘ido akan lamarin a duniya.

Sakatare Janar na MDD Ban ki moon
Sakatare Janar na MDD Ban ki moon REUTERS/Stringer
Talla

Daraktar Hukumar Jose Graziano da Silva, ta ce a yanzu haka akwai mutane miliyan 167, da suka rabu da yunwa, yayyin da ake da adaddin miliyan 795 da ke cikin matsananci yunwa, kuma mafi yawa daga cikin wannan alkalluma, sun fito ne daga yankuna Afrika da Asia da kuma latin Amurka.

Graziano da Silva ta ce Rashin dai-daito tsakanin al’umomi, batun Siyasa da rashin kwanciyar hankali da ake fama dasu a  wasu yankuna, da kuma sauyin yanayi na daga cikin abubuwa da ke taka muhimmiyar rawa wajen Jefa al’ummah acikin halin yunwa.

Graziano da Silva ta kuma bayyana cewa, acikin kasashen 72 cikin 129 da hukumar ta sa wa ido, sun yi namiji kokarin wajen dakile yunwa da kuma rashin cin abinci mai inganci.

Majalisar dinkin duniya, dai ta ce wannan kyawawa alkallumar data samu a wannan lokaci, akwai yiwuwar cewa na bada jimawa ba za’a kawar da matsalar yunwa a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.