Isa ga babban shafi
Nepal

Jami’an agaji na fuskantar matsaloli a Nepal

Masu aikin ceto na ci gaba da kokarin kai dauki a kasar Nepal bayan wata girgizan kasa mai karfin maki 7.3 ta sake abkawa kasar a jiya Talata, inda ta haifar da zabtarewar kasa tare da rusa gine gine a gabacin kasar. Sai dai akwai wani jirgin Sojin kasar Amurka mai saukar Angulu da ya yi batan dabo a yayin da jirgin ke kokarin kai agaji a Nepal.

Sojoji na aikin ceton mutanen da girgizan kasar Nepal ta shafa.
Sojoji na aikin ceton mutanen da girgizan kasar Nepal ta shafa. REUTERS/Navesh Chitrakar
Talla

Mutane da dama ne aka ruwaito sun mutu a girgizan kasar da ta sake abkawa gabacin Nepal bayan mummunar girgizan kasar da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 8,000 a makwanni biyu da suka gabata.

Girgizan kasar ta shafi yankin tsaunin Everest zuwa cikin India da kuma yankin kabilar Tibet a China.

Ma’aikatar cikin gida a kasar tace adadin mutane 65 suka mutu zuwa yanzu amma sama da dubu daya ne suka samu raunika, yayin da kuma girgizan kasar ta kashe akalla mutane 17 a arewacin India.

Yanzu haka kuma sojojin Nepal sun shiga aikin lalubo jirgin Sojin Amurka da ya bata da ke aikin agaji zuwa gabacin Nepal inda girgigzan kasar ta shafa.

Hukumar samar da tallafin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tace suna fuskantar kalubale wajen kokarin shiga yankin da girginzan kasar ta shafa a gabacin Nepal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.