Isa ga babban shafi
Amurka

MDD ta nemi Amurka ta diba matsalar wariyar fata

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci hukumomin kasar Amurka su binciki zargin da ake y iwa ‘Yan sandan kasar na nuna wariyar fata, a daidai lokacin da ake ci gaba da tarzomar nuna adawa da matakin da alkalan kotu suka dauka na wanke Dan sanda farar fata da ya kashe Micheal Brown bakar fata a birnin Fergusson.

'Yan sandan Amurka da ke arangama da masu zanga-zangar adawa da su a Ferguson
'Yan sandan Amurka da ke arangama da masu zanga-zangar adawa da su a Ferguson REUTERS/Mario Anzuoni
Talla

Sanarwar da Ofishin kula da kare hakkokin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar ta bayyana cewa akwai bukatar sake bitar wasu daga cikin dokokin kasar ta Amurka domin tabbatar da cewa sun dace da zamani, a daidai wannan lokaci da jama’a ke ci gaba da tarzoma a birane daban daban na kasar.

Shugaban Ofishin Zeid Ra’ad Alhussein, ya bayyana a wata sanarwa cewa, ya damu matuka dangane da yadda sau da dama ‘yan sanda farar fata ke bindige bakake a Amurka, amma kuma ba abin da ke faruwa ga wadanda suka aikata hakan, yayin da a daya bangare gidajen yarin kasar suka cika makil da bakeke tare da yanke wa da dama daga cikinsu hukuncin kisa.

Ministar shari’a ta Faransa wadda ke da nasaba ta asali da bakar fata Christine Taubira, ta diga ayar tambaya ne a shafinta na Tweeter, tana mai cewa ko saboda me aka kashe Brown mai shekaru 18, da Trayyon Martin mai shekaru 17 da Tamir Rice mai shekaru 12 da dai sauran mutanen da ‘yan sandan na Amurka suka kashe a irin wannan yanayi?

Lauyan iyalan Micheal Brown mai suna Darren Wilson, ya bayyana matakin da masu bincike na kotu suka dauka na wanke dan sandan da ya harbe wanda ya ke karewa a matsayin rashin adalci.

Tuni dai Obama ya bukaci Amurkawa su kai zuciya nesa tare da gudanar da zanga-zangar lumana don kwato ‘yancin kisan Brown.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.