Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

An caccaki Rasha a taron kungiyar G20 da aka yi a Australiya

Yau lahadi shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya fice daga kasar Australia, bayan da aka kammala taron kungiyar kasashe masu arzakin ta G20, inda rai yabaci sakamakon caccakar da aka yi masa kan rikicin kasar Ukraine. Shugaba Putin ya fice daba taron ne kafin a fidda sanarwar bayan taron, sai dai ya halarci liyafar cin abincin da aka shirya kafin kammala taron, inda ya yaba da yadda aka tattauna muhimman batutuwa.A wani bangaren kuma kasashen Amurka, Autraliya da Japan sun nemi Rasha ta daina tsama baki a karkokin cikin gidan kasar Ukraine, inda kuma suka nemi a ayi adalci ga wadanda suka rasa ransu a hadarin jirgin kasar Malaysia, da ake zargi ‘yan tawayen Ukraine masu goyon bayan Rasha ne suka harbo shi.Bayan taron da suka kammala, a gafen taron kasashen masu karfin tattalin arziki na G20, Shugabannin kasashen 3 sun kuma bayyana adawa da matakan da suke gani Rasha dauka, na haddasa rikici a Gabashin Ukraine. 

Shugaban Rasha Vladimir Poutine lokacin da yake ficewa daga taron G20
Shugaban Rasha Vladimir Poutine lokacin da yake ficewa daga taron G20 REUTERS/Jason Reed
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.