Isa ga babban shafi

Kungiyar Oxfam tace bambanci tsakanin attajirai da talakawa na karuwa a duniya

Kungiyar agaji ta Oxfam ta fitar da rahoton dake cewa yawan mutanen da suka mallaki biliyoyin Dala sun karu a duniya, tun bayan matsalar tattalin arzikin da aka samu a duniya. Sai dai kungiyar, dake kasar Britaniya ta koka, kan yadda ake ci gaba da samun banbanci tsakanin masu arziki da talakawa.Daraktar gudanarwan kungiya ta Oxfam Winnie Byanyima, tace dukiyar wasu tsirarun al’ummar duniya na karuwa kuma zata ci gaba da karuwa har sai gwamnatoci sun dauki mataki.Rahoton da kungiyar ta fita, yace maimakon samar da ci gaba tattalin arziki, banbancin na matsayin wani gagarumin shingen da zai iya hana ci gaba tsakanin al’ummar duniya da dama.Rahoton yace banbancin da ake samu tsanin kasashen duniya ya ragu a cikin shekaru 14 da suka gabata, amma kuma lamarin ba haka yake ba a cikin kasashe, inda talkawa ke cin kwakwa, yayinda makwabtansu ke fantamawa.Rahoton ya kara da cewa kashi 70 cikin 1001 na al’umma suna zaune ne a kasashen da banbanci tsakanin masu shi da talakawa ke ci gaba da fadada cikin shekaru 30 da suka gabata.Kungiyar tace a kullu yaumin arzikin mutane 85 da suka fi wadata a duniya na karuwa da kusan dalar Amurka Miliyon 700.Don haka Oxfam ta nema shugabanni a kasashen duniya su dauki mataki kan lamarin, dake matsayin babbar barazana. 

Takardun kudin EURO
Takardun kudin EURO REUTERS/Thomas Peter
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.