Isa ga babban shafi
NATO

Birtaniya ta fice Afghanistan

Sojojin Birtaniya sun mika ragamar tafiyar da sansaninsu na karshe ga Sojojin Afghanistan, wanda ya kawo karshen aikin Sojojin kasar na tsaro bayan shafe shekaru 13 suna yaki da Taliban a Afghanistan.

Sojojin Amurka na sassauta Tutar kasar a sansaninsu da ke Helmand a Afghanistan
Sojojin Amurka na sassauta Tutar kasar a sansaninsu da ke Helmand a Afghanistan REUTERS/Omar Sobhani
Talla

An sassauta tutar Birtaniya a Sansanin na karshe wanda ke a lardin Helmand.

A cikin watan Disemba ne na wannan shekarar dukkanin dakarun Kungiyar tsaro ta NATO zasu fice Afghanistan, inda Sojoji da ‘Yan Sandan Afghanistan zasu ci gaba da tafiyar da sha’anin tsaro da tunkarar Mayakan Taliban.

Jimillar Sojojin Birtaniya 453 aka kashe a yakin Afghanistan, yayin da aka kashe Sojojin Amurka 2,349.

Ministan harakokin tsaron Birtaniya Michael Fallon ya jinjinawa kasarsa ga irin shekarun da ta kwashe tana fada da Taliban

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.