Isa ga babban shafi
Falesdinu-Isra'ila

kashi 80 cikin 100 na Falesdinawa na bukatar ci gaba da kai wa Israila harin roka

WANI bincike da aka gudanar ya nuna cewar akasarin Falasdinawa na goyan bayan ci gaba da harbawa Israila rokoki daga Gaza muddin taki cire takunkumin da kakabawa Yankin.

REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Binciken da Cibiyar dake kula da manufofin Falasdinawa ta yi ya nuna cewar kashi 80 na mutanen da aka ji ra’ayoyinsu sun bukaci cire takunkumin ko kuma cigaba da harba rokokin a yayin da kashi 44 suka ce, ta hanyar anfani da makami ne kawai Israila zata amince da bukatar su, sabanin kashi 29 dake bukatar ci gaba da tattaunawa.

Yanzu haka dai kasar Israila ta yi tsayin gwamin jaki a tattaunawar da take yi da Palastinawa karkashin shiga tsakanin kasar Masar, cewa sai palastinawa sun ajiye makamai kafin ta amince da wasu bukatun nasu, matakin da kungiyar Hamas t ace da sake ba zata taba amin cewa da hakan ba, al’amarin da ake ganin zai kai tattaunawar ga watsewa ba tare da cimma wani abin kirki ba

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.