Isa ga babban shafi
Kungiyar Tarayyar Turai

EU ta bukaci a kara maida hankali ga yaduwar Ebola

Kungiyar tarayyar Kasashen Turai ta gargadi kasashen Duniya da su gaggauta kai dauki ga wasu kasashen yammancin Afrika da yanzu haka ke yakar cutar Ebola da mai ci gaba da lakume rayukan mutane. Wannan kuma ya biyo ne bayan kiran da Majalisar Dinkin Duniya ta yi game da yadda cutar ke ci gaba da yaduwa

European flags are seen outside the European Commission headquarters in Brussels September 10, 2014.
European flags are seen outside the European Commission headquarters in Brussels September 10, 2014. REUTERS/Yves Herman
Talla

Bayan kwashe watanni da ballewar cutar, yanzu Kungiyar kasashen turai ta fara nuna yunkurinta wajan yaki da Cutar Ebola.

Kwamishiniyar Hukumar bada agajin gagawa ta kungiyar Kristalina Georgieva ta bayyana takaicinta na jinkirin da kasashen duniya suka yi dangane da taimakon yankunan da cutar ke addaba a halin yanzu.

Sakomakon haka, hukumar da take shugabanta, ta saki kudi sama da Euro miliyan 150 don yaki da cutar, ta kuma yi kira da babban murya ga sauran kasashe da su tallafa ta hanyar bayar da kudi.

Nan gaba ana sa ran shugaba Barack Obama na Amurka zai umarci majalisar zartaswa ta kasar da ta saki dala miliyan 88 a matsayin tallafi don yakar cutar a yankunan da matsalar ta yi kamari.

Tun bayan bullar Ebola a farkon wannan shekarar, mutane sama da 2000 ne suka rasa rayukan su yayinda kalilan suka tsallake Rijiya da baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.