Amurka ta yi kira ga Putin akan Ukraine
Sakataren harakokin Wajen Amurka John Kerry ya nemi kasar Rasha ta dauki dukkan matakan da suka wajaba domin hana masu tayar da kayar baya da ke kasar Ukraine ci gaba da hardasa husuma a kasar.
Wallafawa ranar:
John Kerry wanda ya ke Magana bayan taron Ministocin Waje na kungiyar tsaro ta NATO, da aka yi a Brussels, yace shugaban Rasha Vladmir Putin dole ya kira ‘yan tawayen Ukraine da ke samun goyon bayan Rasha, da su ajiye makamansu, tare da yanke dukkan gudunmawa da Rasha ke ba su.
Shugabannin kungiyar kasashen Turai duk sun yi irin wannan kira ga kasar Rasha, domin a kawo karshen rikicin da ake samu a Ukraine mai yawan mutane miliyan 46.
Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya yi barazanar kaddamar da wani mataki na soji, bayan da ‘yan tawayen kasar suka kashe wasu dakarun kasar guda Tara.
Wannan kuma ke nuna muraran cewa babu batun sulhu da ‘yan tawayen da ke ci gaba da yakin sari-ka-noke, na tsawon makonni 11, da ya kai ga rasa rayukan mutane 435.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu