Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Putin ya nema 'yan Majalisu su janye batun mamaye Ukraine

A wani mataki mai cike da ban mamaki, shugaban kasar Rasha Vladmir Putin, ya nemi ‘yan majalisun kasar da su janye damar da suka bashi na ya mamaye kasar Ukraine, matakin da hukumomin kasar Ukraine suka nuna gamsuwarsu akai. 

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Alexei Druzhinin/RIA Novosti/Kremlin
Talla

Wannan mataki da Putin ya dauka na zuwa ne bayan barazanar tsaurara takunkumai da kasashen yammaci suka ce za su akan kasar.

A farkon watan Maris ne ‘yan majalisun suka baiwa Putin damar tura dakaru zuwa kasar ta Ukraine, a wani yunkurin daidaita al’amura da suka rincabe a gabashin kasar.

Tuni dai sabon shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko ya yi lale marhabun da wannan mataki na Rasha, wanda ya bayyana a matsayin “matakin farko da shugaban Rasha ya dauka a karon farko, na ganin an shawo kan rikicin kasar.”

Dama dai Rasha ta jibge dakarun ta a kan iyakarta da Ukraine a cikin shirin ko ta kwana.

Sai dai duk da wannan bukata da Putin ya mikawa majalisar kasar, shugaban ya ce ba zai zira ido yana kallo ana muzgunawa ‘yan asalin Rasha dake zaune a agbashin kasar ta Ukraine ba.

“A ko da yaushe, za mu kare ‘yan kasarmu a gabashin Ukraine.” Inji Putin.

Putin ya kuma kara nanata cewa wa’adin tsagaita wuta da aka shata na tsawon kwanaki bakwai ya yi kadan.

Wannan kuma na faruwa ne yayin da rahotanni ke cewa duk wannan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma, a yau Talata, magoya bayan Rasha sun kakkabo wani jrgin saman dakarun Ukraine, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dakaru tara.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.