Isra'ila na cin zarafin fararen Hula inji Amaruka
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana Isra’ila a matsayin kasar dake taka gagarumar rawa wajen fada da ayyukan ta’addanci a Duniya, To sai dai rahoton na bana ya bayyana cewa Israel ta aikata ayyuka na asha har guda 399, wadanda ake iya fassarawa a matsayin ta’addanci.Rahoton ya bayar da misali da abinda masu tsatsauran ra’ayin yahudancin a Isra’ila ke aikatawa da suka hada da kai hare-hare kan fararen hula, da lalata kadarorinsu, sannan kuma da rusa masallatai har ma da mujami’u ko dai a yankin Palasdinawa na yammacin kogin Jordan ko kuma a birnin Quds.
Wallafawa ranar:
Duk da yake hukumomin Tel Aviv sun kafa runduna ta musamman domin bincike da kuma yiyuwar hukunta wadanda ke aikata irin wadannan laifufuka, to amma hakan bai wadatar ba a cewar rahoton, kuma dole a kira wannan ta’asa a matsayin ta’addanci.
Tuni dai rundunar ‘yan sandan Isra’ila ta mayar da martani dangane da wannan zargi, inda mai magana da yawunta Michy Rosenfeld ke cewa ba ta yadda za a danganta wadannan hare-hare da yahudawan ke kai wa Falasdinawa a matsayin ta’addanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu