MDD ta bukaci Fadar Vatican ta mika masu yin lalata da Yara ga ‘Yan sanda
Hukumar kare kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci fadar Vatican ta Fafaroma ta tube Malaman Darikar Katolika daga mukaminsu wadanda ake tuhuma da yin lalata da kananan yara tare da mika su ga ‘Yan sanda.
Wallafawa ranar:
Kwamitin da aka nada domin gudanar da bincike akan matsalar ya yi suka ga sabbin tsare tsaren da Fadar Vatican ke aiwatarwa domin ba masu yin lalata da kananan yara damar ci gaba da gudunar da mummunar tabi’ar ta lalata rayuwar dubban kananan yara.
Hukumar ta kuma zargi Fadar Vatican akan yadda take tunkarar mu’amular jinsi da zubar da ciki.
Akwai kwamiti da Fadar Vatican ta kafa domin yaki da matsalar lalata da kananan yara a darikar Katolika kuma ana sa ran zasu fitar da sanarwa akan rahoton.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa akan yadda fadar Vatican ke jan kafa wajen yaki da matsalar cin zarafin kananan yara musamman tsakanin manyan Limaman darikar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu