Isa ga babban shafi
2014

Shugabannin duniya sun yi jawabin sabuwar shekara

A kasashen duniya daban daban an gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekara ta 2014 inda shugabannin kasashe suka gabatar da jawabai, yayin da milyoyin mutane suka shaidi yadda shekarar ta kama a sassan kasashen duniya.

Bukukuwan sabuwar shekara ta 2014
Bukukuwan sabuwar shekara ta 2014 REUTERS/Tyrone Siu
Talla

Birnin Dubai a Daular Larabawa yana neman samun lambar yabo ta 2014 saboda yadda aka kawata garin da harba kayan wasan wuta sama da 400,000 inda mutane suka yi cincirindo suna daukar hoto a dogon bene mafi girma a duniya na Burj Khalifa.

A 2011 kasar Kuwait ce ta samu lambar yabo ta kamfanin Guinness bayan kwashe sa’o’I ana harba kayan wasannin wuta sama 77,282.

A kasar Ukraine dai masu hamayya da shugaban kasar da yawansu ya kai dubu dari biyu ne suka taru a tsakiyar birnin Kiev a cikin daren sabuwar shekara, inda suka jaddada bukatar ganin kasarsu ta kulla kawance da kungiyar Tarayyar Turai.
A kasar Rasha inda ake da bambancin awowi 8 tsakanin bangaren gabashi da na yammaci, an watsa jawabin shugaba Vladamir Putin ne har sau biyu a daidai lokacin da jama’a ke shiga sabuwar shekarar.

Shugaba Francois Hollande na Faransa kuwa, wanda ya gabatarwa al’ummar kasar da wani jawabi mai tsawon mintuna 10, ya fi mayar da hankali ne a game da manyan manufofin gwamnatinsa na tattalin arziki.

Jacob Zuma na kasar firka ta Kudu a na sa jawabi ya yi kira ne ga al’ummar kasar da su yi riko da koyarwa irin ta tsohon shugaban kasar marigayi Nelson Mandela, yayin da shugaban kasar Cote D’Ivoire Alassane Ouattara ya bayyana aniyarsa ta sakin wasu daga cikin magoya bayan tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo tare da bai wa wadanda ke gudun hijira damar komawa gida.

A Tarayyar Najeriya kuwa bukukuwa biyu ne ake gudanarwa, da suka hada da shiga sabuwar shekara da kuma cika shekaru 100 da hadewar yankin arewaci da kudancin kasar.

A jawabinsa na sabuwar shekara, Shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan ya fitar da wani sako zuwa ga al’ummar Najeriya dangane da shiga sabuwar shekara ta 2014, inda a cikin ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da ya ce gwamnatinsa ta samu a shekarar da ta gabata, da batun tsaro da yaki da rashawa da dai sauran batutuwa da dama da suka addabi Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.