Brazil
Paparoma Francis na ziyara a garin Aparecida na kasar Brazil
Paparoma Francis, wanda ke ci gaba da ziyarar aiki a kasar Brazil, ya bukaci matasa a wannan zamani da su kaucewa son kudi da kuma son mulki, saboda da a cewarsa su ne abubuwan da ke ruda mutum har ma ya kaucewa hanyar bautawa Ubangijinsa.
Wallafawa ranar:
Talla
Paparoma wanda ke gudanar da ziyara ta farko a matsayinsa na shugaban Cocin Katolika a kasar ta Brazil, a yau laraba ya kai ziyarar ne a Apare-cida, yankin da mabiya darikar katolika ke dauka da matukar muhimmanci, inda ya gabatar da jawabi a gaban dubban matasa..
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu