Fafaroma ya gabatar da jawabin karshe kafin yin ban kwana da fadar Vatican
Mabiya Addinin kirista sun hada gangami a dandalin St Peters a fadar Vatican domin sauraren jawabin Fafaroma Benedict na Goma sha Shida kafin ya yi Murabus a ranar Alhamis. Fafaroma shi ne shugaban Mabiya Darikar Katolika a duniya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tun wayewar safiya ne dubban mabiya suka fara hada gangami domin yin ban kwana da Fafaroma mai shekaru 85 a duniya.
Akalla mutane 50,000 ne suka yanki tikiti domin sauraren jawabin na Fafaroma.
Benedict na sha shida zai ci gaba da amfani da Sunan Fafaroma amma mai murabus.
Fafaroma Benedict shi ne mutum na biyu da ya yi murabus da kansa tun lokacin Fafaroma Gregory na Sha Biyu da ya yi murabus a shekarar 1415.
Sai dai wannan bukin na zuwa ne a dai dai lokacin da wani limamin mabiya Darikar Katolika a Birtaniya ke fuskatar tuhuma bisa yin lalata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu