Isa ga babban shafi
Venezuela

An ajiye gawar Chavez a Caracas domin girmama shi

An ajiye Akwatin gawar Shugaban kasar Venezuela, Hugo Chavez a wata cibiyar Soji da ke birnin Caracas domin girmama shi bayan an kewaya da gawar a sassan yankunan birnin. Hugo Chavez ya mutu ne bayan fama da cutar Cancer.

Christina Kirchner da Jose Mujica da Evo Morales Shugaban kasashen Latin Amurka suna girmama gawar Shugaban Venezuela Hugo Chavez
Christina Kirchner da Jose Mujica da Evo Morales Shugaban kasashen Latin Amurka suna girmama gawar Shugaban Venezuela Hugo Chavez Reuters
Talla

Dubban mutane ne a kasar suka fito domin karrama gawar Shugaban dauke da tutar kasar bayan dauko gawar Chavez daga asibitin da ya mutu.

Mataimakin shugaban kasar ne Nicolas Maduro, ke jagorancin zaman makokin mutuwar Chavez a kasar Venezuela.

Mahaifiyar Chavez, Elena, ita ce ke wa gawar shugaban rakiya, inda ta rufe fuskarta da farin hankacif tare da ‘yayan shugaban mata guda uku suna shatata kuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.