Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya nemi hadin kan Amurkawa bayan rantsar da shi wa’adi na biyu

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi kiran hadin kan Amurkawa bayan rantsar da shi wa’adi na biyu tare da kira ga ‘Yan adawa su ba shi hadin kai wajen ganin ya cim ma kudirin shi game da batun shige da fice da canjin yanayi da kuma dokar mallakar Bindiga.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Mista Obama ya sha alwashin farfado da tattalin arzikin Amurka tare da alkawalin kawo karshen yake yake.

Obama mai shekaru 51 na haihuwa kuma Shugaban Amurka na 44, ya karbi rantsuwar kama aiki ne daga Mai shari’a John Roberts.

Daruruwan Amurkawa ne suka halarci taron rantsar da Obama da suka hada da tsoffin shugabannin kasar Amurka, Bill Clinton da Jimmy Carter.

Obama wanda shi ne Shugaban Amurka bakar fata na farko, ya dafa Lintafin Linjila ne Mallakar Abraham Lincoln Shugaban da ya kawo karshen safarar bayi a Amurka da kuma Littafin Martin Luther King dan rajin kare hakkin bil’adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.