Isa ga babban shafi
Rasha-Birtaniya-Syria

Ziyarar Putin a London

Firaministan Birtaniya David Cameron da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zasu gana da juna domin tattauna rikicin Syria kafin shugabannin su shiga kallon wasan Judo a wasannin Olympics da ake gudanarwa a Birnin London.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin REUTERS/Sergei Karpukhin
Talla

Tuni dai kasar Birtaniya ke kalubalantar kasar Rasha game da bijerewa matakan Majalisar Dinkin Duniya akan Syria inda ake ci gaba da zubar da jini tsakanin dakarun gwamnati da ‘Yan tawaye.

Birtaniya tace ta yi imanin Putin zai kare matsayin Rasha game da rikicin Syria a ziyararsa ta farko zuwa London tun shekarar 2005.

An kwashe lokaci mai tsawo kasar Rasha da China suna hawa kujerar na-ki ga duk wani yunkuri na kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya akan Syria.

David Cameron yana cikin jerin shugabannin duniya da ke kira lalle sai Bashar Assad ya yi murabus amma kasar Rasha ita ce sahun gaba na yin watsi da bukatar kasashen.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.