Isa ga babban shafi
France-Pakistan

An cafke wani Bafaranshe kwamandan al Qaeda a Pakistan

Mahukuntan kasar Pakistan sun ce sun Cafke wani Bafaranshe mai suna Naamen Meziche wanda ake alakantawa da kungiyar al Qaeda da suka jagoranci harin 9/11 da aka kai a kasar Amurka.

Naamen Meziche
Naamen Meziche historycommon.org
Talla

Wani masanin yaki da Ta’addanci yace an cafke Naamen Meziche a karshen watan Mayu akan hanyarsa zuwa Afghanistan a Baluchistan da ke Lardin Qauetta kusa da kan iyakar Pakistan da Iran.

Cafke Naamen Meziche na zuwa ne cikin matsin lambar da Pakistan ke fuskanta daga Amurka game da kungiyar al Qaeda.

Tun lokacin da dakarun Amurka suka kashe Osama Bin Laden a Pakistan danganta ta katse tsakanin Pakistan da Amurka.

Naamen Meziche dan asalin kasar Algeria ne wanda aka Haifa a shekarar 1970, amma rahotanni sun ce yana cikin manyan Mambobin kungiyar al Qaeda da ke bada horo a Arewacin Jamus.

Wani masanin yaki da ta’addanci yace Jami’an leken asirin kasar Faransa sun dade da sanin Meziche yana buya akan iyakar kasashen Afghanistan da Iran da Paksitan

Sai dai a shekarar 2010 akwai rahotanni da suka ce an kashe Meziche a wani harin da dakarun Amurka suka kai a Arewacin Waziristan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.