Isa ga babban shafi
Pakistan

Kotun Pakistan ta dakatar da Gilani, gwamnati za ta nada Sabon PM

Kotun kasar Pakistan ta dakatar da Fira Ministan kasar Yusuf Raza Gilani daga mukamin shi bayan samun shi da laifin keta mutuncinta. Shugaban kasar ya shiga tattaunawa domin nada sabon Fira Minista.

Fira Ministan Pakistan, Yusuf Raza Gilani
Fira Ministan Pakistan, Yusuf Raza Gilani REUTERS/Faisal Mahmood
Talla

Yousuf Raza Gilani, wanda ya karbi mukamin Fira minista bayan Jam’iyya PPP ta lashe zabe a shekarar 2008, kotun tace ta dakatar da mukamin shi ne bayan kin amincewa mahukuntan Switzerland kaddamar da binciken cin hanci da rashawa da ake wa Shugaban kasa Asif Ali Zardari.

Hukuncin kotun ya nuna tankiyar da ake samu tsakanin bangaren gwamnati, da bangaren shari’a a kasar.

Babban alkalin kotun mai Shari’a Iftikar Khaudiri, yace kotun ta yanke hukuncin saboda Fira Ministan ya ki daukaka kara bayan shafe watanni biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.