Isa ga babban shafi
MDD-Koriya ta Arewa

MDD ta karfafa takunkumi ga Koriya ta Arewa

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya sake karfafa takunkumin da ya kakaba wa kasar Koriya ta Arewa, tare da barazanar sake sa wasu sabbin takunkumin, in har kasar sake yunkurin harba rokan ta a sararin samaniya.

A lokacin da Korea ta Arewa zata gwada harba Tauraronta a Sararin samaniya
A lokacin da Korea ta Arewa zata gwada harba Tauraronta a Sararin samaniya RFI/Keo Chhaya
Talla

kwamitin mai membobin kasashe 15, da ya hada da babbar kawar Koriya ta arewan China, yace harba rokan da ta tarwatse bayan harba shi a karon farko ya saba wa kudurin majalisar, tare da Allah waddai da gwajin na ranar Juma’a.

Kwamitin ya bukaci a sake nazarin takunkumin da aka sanya ga kamfanonin da daidaikun mutane ‘yan kasar, don duba yiwuwar rufe asusun ajiyarsu.
Sai dai Koriya ta arewa ba tace uffan kan wannan matakin ba.

Kasar Koriya tace zata harba rokan ne don sanya na’urar ta mai nazari kan yanayi, da zata gewaya sararin samaniya, amma kuma Amurka da kawayen ta sun ce wannan yunkuri ne na gwada makamin ta mai linzami.

China kuma ta nemi a ci gaba da tattaunawa da hukumomin na birnin Pyonyong.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.