Isa ga babban shafi
Syria

Kofi Annan ya kammala ziyara Syria ba tare da samun wani sauyi ba

Kofi Annan Manzo na musamman da Majalisa Dinkin Duniya ta aika Syria, ya kammala ziyarar shi ba tare da kawo karshen rikicin kasar ba bayan ganawa da Shugaba Bashar al Assad. Kuma yanzu haka dakarun gwamnatin Syria na ci gaba da fafatawa da masu zanga-zangar kin jinin Assad.

Koffi Annan, Manzo na Musamman na Majalisar Dinkin Duniya a lokacin da yake ganawa da Shugaban kasar Syria Bashar Al Assad
Koffi Annan, Manzo na Musamman na Majalisar Dinkin Duniya a lokacin da yake ganawa da Shugaban kasar Syria Bashar Al Assad REUTERS/SANA/Handout
Talla

Annan ya mika wa Shugaba Assad taswiwar hanyoyin magance rikicin kasar da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ya yi sanadiyar hallaka fiye da mutane 7000 tun fara zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaban a bara.

 

Kasashen Turai da kungiyar kasashen Larabawa sun dade suna neman hanyoyin kawo karshen zubar da jinni a Syria amma kuma bangaren gwamnatin da ‘Yan adawa dukkaninsu sun yi watsi da matakin sasantawa.

Mista Annan ya bukaci kawo karshen Zubar da jini tare da neman komawa a teburin sasantawa tsakanin ‘yan Siyasar kasar bayan ya gana da Assad a ranar Lahadi.

Sai dai Assad ya shaidawa Kofi Annan cewa salon sasanta rikicin ta hanyar Siyasa ba zai yiyu ba domin yadda wasu  ‘Yan adawa ke barazana ga gwamnatinsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.