Isa ga babban shafi
Faransa-Turkiya-Armenia

Turkiya ta janye jekadanta daga Faransa

Gwamnatin kasar Turkiya ta janye jakadunta daga kasar Faransa tare da katse huldar soji da kasar bayan da majalisar Faransa ta amince da kudirin doka game da gasgata tarihin kisan da dakarun Turkiya suka yiwa Armeniyawa a zamanin Othman a shekarar 1915.

Fira Ministan Turkiya  Recep Tayyip Erdogan
Fira Ministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan Reuters
Talla

Kasar Turkiya ta bayyana jingine huldar sojan da ke tsakaninta da Fransa wace ta zarga da nuna mata kabilanci da wariya, bayan da ‘ yan majalisar dokokin Fransa a jiya alhamis suka kada kuri’ar amincewa da wata doka da taki daukar kisan rashin imanin da dakarun Turkiya suk yi wa Armeniyawa a 1915, a matsayin kisan kare dangi.

Fira Ministan kasar Turkiya Racep Tayyip Erdogan, ya soke ziyarar huldar da ya yi niyyar kai wa a kasar Faransa, tare da kiran jakadan Turkiya gida, domin tattaunawa.

A bangaren Faransa ta bakin ministan harakokin wajenta Alain Juppe, kasar ta nuna matukar bacin ranta dangane da matakin da Turkiyar ta dauka. Mista Juppe ya nemi Turkiya sassauta fushinta dangane da wannan al’amari.

A cewarsa, kasashen Turkiya da Faransa kawayen juna ne na kut da kut, don haka yana da matukar muhimmanci a cikin irin wannan yanayi, su rungumi hanyar tattaunawa, tare da la’akari da huldar da ke tsakanin kasashen, domin warware rashin fahimtar da ke tsakaninsu.

A kasar Faransa an zargin shugaban kasa Nicolas Sarkozy bisa amincewa da kada kuri’ar a zauren Majalisar domin samun kuri’u daga Armeniyawa a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a badi.

Kudirin dokar da zai yi watsi da duk wani haramci na aikata laifukan yaki da gwamnatin kasar Faransa zata amince, za’a gabatar da kudirin dokar a gaban Majalisar dattijan kasar domin neman amincewarsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.