Isa ga babban shafi
Rasha-MDD-Syria

Rasha ta yi Allah waddai da rikicin kasar Syria

A Zauren Majalisar Dinkin Duniya, kasar Rasha ta ba kasashen duniya mamaki inda ta gabatar da wani daftari da ya yi Allah waddai da rikicin kasar Syria tare neman kawo karshen jubar da jini da ake yi a cikin kasar. Da dadewa ne kasashen Yammaci ke kokarin kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya daukar mataki kan Syria amma kasashe China da Rasha suka bijerewa kudirin.

Fira Mnistan Rasha, Vladimir Putin a lokacin da yake jawabi ta kafar Telebijin din kasar
Fira Mnistan Rasha, Vladimir Putin a lokacin da yake jawabi ta kafar Telebijin din kasar REUTERS/Alexei Nikolsky/RIA Novosti/Pool
Talla

Kasar Rasha ta yi kiran gudanar da wani taron gaggawa domin daukar mataki kan Syria tare da nuna damuwa da shigar da makamai da ake yi a cikin kasar

Kasashen Turai da Amurka sun yi maraba da wannan daftarin na Rasha,amma sun yi korafin daftarin bai yi bayani sosai ba akan cin zarafin Bil-adama da gwamnatin Syria ta yi.

Kasashen Sun ce zasu kalubalanci duk wani daftarin da ya kimanata rikicin tsakanin ‘Yan adawa dai dai da Gwamnati.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.