Isa ga babban shafi
Sa'udi Arabia

An fille wa wani dan kasar Sa’udiyya kai bisa laifin kisan kai

Yau talata a ka fille wa wani dan kasar Sa’udiyya kai bisa laifin kisan kai, a birnin Yanbu dake yankin masana’antu na Bahar-maliya.Shi dai Mitaab Al-Sanani ya harbe Nayef Al-Dhabiani da bindiga ne, kamar yadda ma’aikatar harkokin cikin gida ta ba da sanarwa da kamfanin dillancin labaran kasar ya fitar, amma babu cikakken bayani.Wannan haddi shi ne karo na 26 a kasar ta Sa’udi Arabiya cikin wannan shekara, a ta cewar kamfanin dillacin labaran Faransa AFP.  

Ministan harkokin wajen Saudi Arabia Prince Saud al-Faisal da Sakatariyar wajen Amurka Hillary Clinton a birnin Riyadh.
Ministan harkokin wajen Saudi Arabia Prince Saud al-Faisal da Sakatariyar wajen Amurka Hillary Clinton a birnin Riyadh. Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.