Isa ga babban shafi

Adadin mutanen da suka mutu a girgizar kasar Japan ya karu

Gwamnatin Japan ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta afka wa tsibirin Honshu ya karu zuwa mutane 48 daga 4 da ta fara sanarwa, yayin da kuma yawan wadanda suka jikkata ya kai mutane 14.

Wani katafaren gini da girgizar kasa ta jirkitar a birnin Wajima, da ke lardin Ishikawa a kasar Japan. 2 ga Janairu, 2024.
Wani katafaren gini da girgizar kasa ta jirkitar a birnin Wajima, da ke lardin Ishikawa a kasar Japan. 2 ga Janairu, 2024. via REUTERS - KYODO
Talla

Rabin adadin mutanen da suka rasa rayukansu a dalilin girgizar kasar dai sun mutu ne a garin Wajima, inda mummunar gobarar da tashi tare da kone gidaje da dama.

Akwai dai fargabar adadin mamatan ka iya karuwa, kasancewar har yanzu jami’an ceto na ci gaba da laluben wadanda iftila’in na ranar Litinin ya rutsa da su.

A halin da ake ciki, mahukuntan Japan din sun sassauta tsawatarwar gargadin da suka yi kan tsbirin na Honshu da sauran yankunan da ke kusa, sai dai sun gargadi mazauna yankin da aka kwashe da su guji komawa gidajensu, domin kuwa, igiyar ruwan teku za ta iya sake murdawa a kowane lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.