Isa ga babban shafi

Akalla mutane 21 suka mutu a wata mahakar ma'adinan ArcelorMittal a Kazakhstan:

Akalla mutane 21 ne suka mutu a kasar Kazakhstan a wani sabon hatsarin da ya afku a mahakar ma'adinan katafaren kamfanin sarrafa karafa na duniya ArcelorMittal, a cewar hukumomin wannan babbar kasa dake tsakiyar Asiya a ranar Asabar.

Tambarin ArcelorMittal
Tambarin ArcelorMittal AFP/File
Talla

"Gobara ta tashi a mahakar ma'adinan Kostenko, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 21," in ji gwamnatin yankin a cikin wata sanarwar manema labarai, inda ta bayyana cewa "a cikin masu hakar ma'adinai 252 da suka halarta a lokacin da lamarin ya faru, Shugabanin mahakar sun dau matakan gaggawa na ceto ma'aikata da dama inda aka fitar da dama daga cikin ramu,. kusan205 a ne aka dawo da su.

Daya daga cikin kamfanonin ArcelorMittal
Daya daga cikin kamfanonin ArcelorMittal REUTERS - ZOHRA BENSEMRA

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.