Isa ga babban shafi
Myanmar

Guterres da Ban Ki Moon sun bukaci a dau mataki don kawo karshen rikicin Myanmar

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da wanda ya gada Ban Ki Moon sun bukaci gwamnatin kasashen dake Gabashin Asia da su sanya hannu wajen kawo karshen rikicin dake gudana a kasar Myanmar.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. ©REUTERS/Carlo Allegri
Talla

Yayin da yake tsokaci kan rikicin kasar, Ban ya bukaci shugabannin da zasu gudanar da taro na musamman da su dauki matakan gaggawa domin dakile tashin hankalin dake gudana a kasar.

Shima Antonio Guterres yace rawar da shugabannin zasu taka nada matukar tasiri wajen zaman lafiyar yankin, saboda haka yana da muhimmanci su hada kan su wajen tafiya tare.

Ana saran shugaban sojin Myanmar Min Aung Hlaing ya halarci taron wanda zai zama masa ziyara ta farko da zai je kasar waje tun bayan juyin mulkin da yayi sanadiyar kasha mutane akalla 730 sakamakon tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.