Isa ga babban shafi
IS

IS ta tabbatar da mutuwar shugabanta Ibrahim Al-Quraishi

Kungiyar IS ta tabbatar da mutuwar shugabanta Abu Ibrahim Al-Quraishi tare da ayyana Abu Hassan Al Hashemi Al-Quraishi a matsayin sabon shugaba.

Gidan da  Al'Quraishi ya gamu da ajalinsa a yayin wani samame da dakarun Amurka suka kai.
Gidan da Al'Quraishi ya gamu da ajalinsa a yayin wani samame da dakarun Amurka suka kai. © France 24 screengrab
Talla

Mayakan kungiyar sun zake cewa shugaban kungiyar shine shugaban mabiya addinin musulunci, kamar yadda kakakin kungiyar ya bayyana ta cikin wata murya da kungiyar ta fitar.

Bayanai sun ce tsohon shugaban, Al’quraishi ya tashi Bam a jikinsa a yayin wani samame da dakarun Amurka suka kai Syria kamar yadda Amurkan ta bayyana.

Al-Quraishi, shine wanda ya jagoranci kungiyar tun shekarar 2019, dan Kabilar Turken da ke kauyen Tal Afar da ke kasar Iraqi, kuma kafin zaman sa shugaban ya maye gurbin Abu Bakr Al-Baghdadi, wanda shi ma Amurkan ta kashe a 2019.

Duk da cewa babu wani cikakken bayani game da sabon shugaban kungiyar, yana cikin wadanda ke kan gaba a jagororin kungiyar.

Wani rahoton majalisar dinkin duniya ya tabbatar da cewa kungiyar ta IS na da mayaka sama da dubu 10 kuma fiye da kaso 80 na aiki ne a kasashen Iraqi da Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.