Isa ga babban shafi
pakistan-IS

IS ta dauki alhakin harin da ya kashe mutane 56 a masallacin Pakistan

Kungiyar IS ta dau alhakin harin kunar bakin wake da ya yi sanadin mutuwar mutane 56 a wani masallacin mabiya mazahabar Shi’a a birnin Peshawar a jiya Juma’a.

IS ta dau alhakin harin kunar bakin wake na masallacin Pakistan.
IS ta dau alhakin harin kunar bakin wake na masallacin Pakistan. AP - Rahmat Gul
Talla

Kungiyar ta wallafa wani shafinta da ake kira Amaq cewa wani mujahidi ya yi nasara a harin da ya kai wani masallacin ‘yan Shi’a.

Mummunan harin  bam din na zuwa ne a rana ta farko ta wasan kwallon Cricket tsakanin Pakistan da Australia a Rawalpindi kilomita 190 daga gabashin birnin a Peshawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.