Isa ga babban shafi
Pakistan-Ta'addanci

Harin ta'addanci ya hallaka mutane 2 tare da jikkata wasu 22 a Pakistan

Akalla mutane 2 suka mutu yayinda wasu 22 suka jikkata yau alhamis bayan tashin wani bom a Lahore na Pakistan, harin da tuni kungiyar ‘yan awayen BNA ta dauki alhakin kaddamar da shi.

Yankin da harin birnin Karachi ya faru.
Yankin da harin birnin Karachi ya faru. AFP - RIZWAN TABASSUM
Talla

Majiyoyin gwamnatin Pakistan da ke tabbatar da harin na tsakar birnin Lahore cibiyar kasuwancin kasar sun ce wadanda harin ya rutsa da su har da kankanun yaro mai shekaru 9

Tuni kungiyar ‘yan awaren Baloch Nationalist Army guda cikin kungiyoyin tsirarun kabilu da ke tayar da kayar baya ta dauki alhakin harin, kugiyar da ke jagorancin ayyukan ta’addanci tsawon shekaru a kudu maso yammacin Pakistan.

Kakakin ‘yansandan birnin Lahore Rana Arif da ke tabbatar da farmakin ya ce ‘yan ta’addan sun dana bom din a jikin wani babur gab da shagon siyayya na zamani na Anarkali.

Baya ga mutum biyu da kuma wasu 22 da suka jikkata majiyar gwamnatin kasar ta ce bom din ya lalata tarin mashina da kuma tarin kayakin da ke makare a shagon cinikayyar.

Firaminsta Amir Khan ya mika sakon jaje ga wadanda harin ya rutsa da su tare da shan alwashin tabbatar da tsaro.

Yankin Balochistan mai arzikin ma’adinai da ke matsayin mafi girma cikin yankunan Pakistan 4 na da iyaka da kasashen Afghanistan da kuma Iran al’ummar yankin fiye da miliyan 7 na zargin gwamnati da kin raba dai dai a kudaden da ake samu ta bangaren albarkatu dalilin da ya haddasa kungiyoyi masu adawa da gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.