Isa ga babban shafi
Amurka-Asiya

Blinken na rangadi kasashen gabashin Asiya don gyara alakarsu da Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a ya fara wani rangadi a yankin kudu maso gabashin Asiya, inda jiya litinin ya fara ziyararsa a birnin Jakarta na Indonesia wanda ya zo dai-dai da ziyarar wani babban jami'in Rasha a kasar.

Ganawar Anthony Blinken da shugaba Joko Widodo na Indonesia a Jakarta.
Ganawar Anthony Blinken da shugaba Joko Widodo na Indonesia a Jakarta. AP - Agus Suparto
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da cewa Antony Blinken ya isa birnin Jakarta na Indonesia bayan taron ministocin harkokin wajen G7 taron da ya karkare da cecekuce kan Rasha.

Blinken ya gana da shugaban na Indonesia Joko Widodo kuma ya nuna goyon baya ga shugabancin Indonesia a yankin Tekun India da Pacific, a matsayin kasa ta uku mafi karfin dimokiradiyya da mutunta dokokin kasa da kasa.

Hukumomin Indonesia sun tabbatar cewa jim kadan bayan ganawar Joko Widodo da Blinken, shugaban ya kuma karbi bakoncin sakataren kwamitin tsaron Rasha Nikolai Patrushev, wanda ke kusa kusa da shugaban Rasha Vladimir Putin, .

Cikin wata sanarwa ministan harkokin wajen Indonessia Retro Marsudi ta ce tattaunawar Blinken da Widodo ta yi armashi, ta na mai jaddada bukatar kasarta na ganin Amurka ta kara zuba jari a yankin kudu maso gabashin Asiya.

A wannan Talata, ake saran Blinken ya gabatar da jawabi kan "manufar Amurka game da yankin Tekun India da Pacific", wanda ke zama yanki da Amurka da China ke gogayya da juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.