Isa ga babban shafi
Taliban-Rasha

Taliban ta aminta da matsayar da taron Rasha ya cimma kan Afghanistan

Rasha da kasashen tsakiyar Asia sun kulla yarjejeniyar aiki tare da Taliban don tabbatar da tsaro a yankin yayinda suka bukaci sabuwar gwamnatin ta Afghanistan ta yi amfani da saukakan manufofi tare da tabbatar da kiyaye dokokin kare hakkin dan adam.

Wakilan Taliban yayin halartar taron da Rasha ta shirya kan Afghanistan.
Wakilan Taliban yayin halartar taron da Rasha ta shirya kan Afghanistan. AP - Alexander Zemlianichenko
Talla

Kasashen China da Iran da suka halarci taron wanda Rasha jagoranta kan Taliban da ya samu halartar kasashe 10 sun alkawarta aiki tare da kungiyar don yakar IS da nufin tabbatar da zaman lafiya a kasar da ke tsaka da fuskantantar manyan matsaloli.

Sai dai taron ya ja hankalin Taliban wajen ganin ta tafiyar da mulki a wannan karon da saukakan manufofi a ciki da wajen kasar baya ga mutunta dokokin kasa da kasa da kuma gyatta alaka tsakaninta da makwabta.

Tuni dai Taliban ta aminta da batutuwan da taron ya tattauna akai sai dai mahalarta tarons un bayyana shakku kan yadda lamurran mata za su tafi cikin kasar ta Afghanistan karkashin mulkin na Taliban.

Taliban a jawabin wakilcinta gaban taron ta sha alwashin tabbatar da ‘yancin mata da na tsiraru da ke arewaci baya ga kin goyon bayan duk wani aikin ta’addanci.

Sai dai kalaman na Taliban kan kin goyon bayan duk wani yunkurin ayyukan ta’addanci ya gamu da kakkausar suka musamman bayan kalaman ministan cikin gidanta Sirajuddin Haqqani da ya bayyana wasu da suka kai harin kunar bakin wake a matsayin gwarazan musulunci.

Taron na Rasha ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kafa kwamitin samarwa da Afghanistan kudaden tafiyar da gwamnati bayan matsain da ta fada tun bayan karbe ikon Taliban da ya sanye katse tallafin kasashen Duniya da kuma kulle asusun ajiyar kasar na ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.