Isa ga babban shafi
Taliban-Afghanistan

Red Cross ta yi gargadin yiwuwar durkushewar sashen lafiya na Afghanistan

Kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa Red Cross ta yi gargadin cewa tsarin kiwon lafiyar kasar Afghanistan yana gaf da durkushewa, sakamakon rufe cibiyoyin kiwon lafiya fiye da dubu 2,000 a duk fadin kasar da ke fama da rikici.

Wani asibiti a Afghanistan.
Wani asibiti a Afghanistan. NOORULLAH SHIRZADA / AFP
Talla

Kungiyar ta Red Cross ta yi kashedin cewa matsanancin karancin kudi na kokarin jefa bangaren lafiya na Afghanistan a cikin hatsari.

Daraktan kungiyar a yankin Asiya da Pacific, Alexander Matheou ya ce ma’aikata na iya jure aiki ba tare da albashi ba na ‘yan makwanni, to amma da zarar magunguna sun kare babu wani taimakon da za a iya bayarwa ga mara lafiya.

Kungiyar ta ce fiye da ma’aikatan lafiya dubu 20 ne suka daina aiki, ko kuma su ke aiki ba tare da albashi ba, kuma dubu 7 daga cikinsu mata ne.

Ko a makon da ya gabata, sai da hukumar lafiya ta duniya ta yi kashedin cewa kasa da rabin asibitocin da ke Afghanistan ne ke aiki, kuma hakan zai iya kawo cikas a yakin da ka da annobar Corona.

Bayan yaki da ta yi fama da shi na kusan shekaru 20, tattalin arzikin Afghanistan ya samu nakasu tun bayan da kungiyar Taliban ta dare karagar mulkin kasar a watan da ya gabata a tsakankanin takunkumai da kuma dakile taimakon da ke isa kasar daga waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.