Isa ga babban shafi
Iran - coronavirus

Adadin mutane da korona ta kashe a Iran ya zarta dubu 100

Adadin mutanen da annobar korona ta kashe a kasar Iran ya zarta dubu 100 a wannan Alhamis, adaidai lokacin da kasar ke kara tsaurar matakan hana bazuwar cutar.

Dakin gobe da nisa na masu dauke da korona a kasar Iran
Dakin gobe da nisa na masu dauke da korona a kasar Iran AFP - KOOSHA MAHSHID FALAHI
Talla

Cikin sa’o’I 24 da suka gabata kadai, kasar ta samu sabbin wadanda cutar ta kashe har 564 cikin sama da mutane dubu 31,266 da suka harbu.

Yanzu haka jumular wadanda ke dauke da cutar ta Covid – 19 a Iran ya kai miliyan 4,587,683 yayin da dubu 100,255 suka mutu, tun bayan bullar cutar a shekarar 2019 a kasar China zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.