Isa ga babban shafi
Afghanostan-China-Taliban

Ministan harkokin wajen China ya gana da manyan jami’an Taliban

Tawagar manyan jami’an kungiyar Taliban na gudanar da ziyarar yini biyu a birnin Beijing don ganawa da mahukuntan China a daidai lokacin da lamurran tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a Afghanistan bayan janyewar dakarun Amurka da na kungiyar Nato daga kasar.

Mataimaikin shugaban TalibanMullah Abdul Ghani Baradar (a tsakiya)
Mataimaikin shugaban TalibanMullah Abdul Ghani Baradar (a tsakiya) Karim Jaafar AFP/Archivos
Talla

Tawagar da ta kunshi mutane 9 na karkashin jagorancin Mullah Abdul Ghani Baradar ne, mataimakin shugaban kungiyar Taliban, tuni ta gana da ministan harkokin wajen China Wang Yi da wasu manyan jami’an diflomasiyya na kasar.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP a birnin Kabul, mai magana da yawun Taliban Mohamad Naeem, ya ce tabbas an yi ganawar to sai dai bai bayyana wurin da aka yi ta ba a cikin kasar ta China.

Naeem ya ce a lokacin ganawar, Taliban ta tabbatar wa China cewa kungiyar ba za ta taba bai wa wani gungu mutane damar yin amfani da Afghanstan don cutar da wata kasa ba.

China dai na da doguwar iyaka da Afghanistan, abin da ya sa mahukuntan Beijing ke nuna fargaba a game da yiyuwar masu tsatsauran ra’ayiza su iya yin amfani da yanayin da ake ciki a Afghanistan don wargaza sha’anin tsaronta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.