Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Afghanistan: Shugaban Taliban ya yi na'am da tattaunawar zaman lafiya

Shugaban kungiyar Taliban Hibatullah Akhundzada ya bayyana goyon bayansa ga batun sulhunta rikicin Afghanistan a siyasance, duk da cewa kungiyar mai tsananin ra’ayin addini ta kaddamar da hare hare a fadin kasar.

Wakilan Taliban a taron zaman lafiya a Doha.
Wakilan Taliban a taron zaman lafiya a Doha. KARIM JAAFAR AFP
Talla

 Akhundzada ya ce duk da nasarar da kungiyarsa ke samu a halin yanzu,  ta yi na’am  da warware rikicin cikin ruwan sanyi, kuma za ta yi amfani da duk wata dama ta kafa daular Musulunci a Afghanistan.

Sanarwar ta sa na zuwa ne a daidai lokacin da wakilan bangarorin da ke kai ruwa rana ke taron lalubo zaman lafiya a birnin Doha, lamarin da ke bada kwarin gwiwar cewa an farfado da tattaunawar da aka fara tsakaninsu tun da farko

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.