Fafaroma Francis ya fara ziyarar kwanaki 4 a Thailand
Shugaban Mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis, ya fara ziyarar Thailand da zuwa wani wurin ibadar Budha domin ganawa da shugaban su.
Wallafawa ranar:
Cikin ayyukan da Fafaroman zai yi sun hada da ganawa da shugaban kasa da Firaminista da kuma gudanar da addu’oi a bainar jama’a wadda ake saran dubban mutane su halarta
.
Francis ya gana da shugaban addinin Budha a yau Alhamis a wani wurin bautarsu dake birnin Bangkok a ziyarsa ta nahiyar Asiya don habaka dangantaka tsakanin addinai.
Wannan ce ziyarar shugaban darikar Katolikan ta farko a kasar Thailand wacce mabiya addinin Budha ne suka fi rinjaye, daga nan ne kuma zai garzaya Japan a ranar Asabar,bayn ya jagoranci sujadar dubban mabiya Katoloika a fadin kudu maso gabashin Asiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu