Isa ga babban shafi
Myanmar

Fafaroma Francis ya isa Myanmar

Shugaban mabiya Darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya gana da babban Hafson sojin kasar Myanmar, a ziyarar da ya fara yau zuwa kasar mai rinjayen mabiya addinin Budda, wadda kuma yanzu haka ke ci gaba da fuskantar suka daga kasashen duniya kan cin zarafi da kisan gillar da su ke yiwa tsirarun Musulmi ‘yan kabilar Rohingya da ke kasar.

Shugaban Mabiya addinin Kirista Fafaroma Francis jim kadan bayan isar sa filin Jirgin saman Yangon babban birnin Myanmar don tattaunawa kan kisan kiyashin da aka yiwa musulmi 'Yan kabilar Rohingya.
Shugaban Mabiya addinin Kirista Fafaroma Francis jim kadan bayan isar sa filin Jirgin saman Yangon babban birnin Myanmar don tattaunawa kan kisan kiyashin da aka yiwa musulmi 'Yan kabilar Rohingya. Reuters Media Express
Talla

Da safiyar yau ne dai daruruwan yara daga kabilu daban daban sanye da kayan gargajiya rike da furanni suka tarbi shugaban na Mabiya addinin Kirista Fafaroma Francis a filin jirgin saman Myanmar da ke Yangon babban birnin kasar baya ga manyan jami’an gwamnatin kasar da suka karbe shi a hukumance.

Bayan Isowar Fafaroman ne kuma ya yi wata ganawa ta musamman da babban Hafson sojin kasar, Janar Min Aung Hlaing a masaukinsa da ke birnin na Yangon, inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro dama zargin da ake kan jami’an sojin kasar na muzgunawa musulmi ‘yan kabilar Rohingya.

A gobe Talata ne kuma ake saran Fafaroman zai yi wata ganawa ta musamman da shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi wadda kima da martabarta ke kara zubewa a idon duniya bayan da ta gaza tabuka abin kirki kan kisan da ake yiwa Musulmi ‘yan kabilar Rohingya.

Manufar ziyarar ta kwananaki hudu da Fafaroma Francis ke gudanarwa ita ce jan hankali ga mabanbantan addinai da kabilun da ke kasar ta Myanmar don samar da zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.