Isa ga babban shafi
Afghanistan

Afghanistan: Mahara sun kaiwa ofishin mataimakin shugaban kasa hari

Akalla mutane 20 suka mutu, yayin da wasu sama da 50 suka samu raunuka, lokacin da aka kai wani hari kan ofishin mataimakin shugaban Afghanistan Amrullah Saleh, a daidai lokacin da ake fara yakin neman zaben shugaban kasar.

Wasu yara a yankin da mahara suka kai farmaki kan ofishin mataimakin shugaban kasar Afghanistan. 29/7/2019.
Wasu yara a yankin da mahara suka kai farmaki kan ofishin mataimakin shugaban kasar Afghanistan. 29/7/2019. Reuters
Talla

Rahotanni sun ce an kaddamar da hare-haren ne da misalin karfe 4 da minti 40 na yamma, lokacin da aka fara jin karar wata fashewa kusa da ofishin mataimakin shugaban kasar, yayin da maharan suka bude wuta kan jama’a.

Bayan kwashe sa’o’i 6 ana dauki ba dadi, jami’an tsaro sun kashe maharan, yayin da suka ceto mutane kusan 150 da suka makale a cikin ginin.

Har zuwa lokacin wallafa wannan labari babuwata kungiya da ta yi ikirarin kai harin.

Harin baya bayan nan na zuwa ne yayin da tattaunawa tayi nisa tsakanin Amurka da shugabanin mayakan Taliban don kawo karshen yakin da aka shafe shekaru akalla 17 ana gwabzawa, da yayi sanadin rasa dubban rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.