Isa ga babban shafi
China-Hong Kong

Matasan Hong Kong sun kai wa ofishin China hari

Akalla mutane dubu 400 gabili matasa, sun gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati a Hong-Kong, inda suka rika jifan ofishin jakadancin China da kwayaakwai domin ci gaba da nuna rashin amincewarsu kan katsalandan din China kan harkokin shari'ar yankin.

Masu zanga-zangar sun yi arangama da jami'an tsaron Hong Kong
Masu zanga-zangar sun yi arangama da jami'an tsaron Hong Kong LAUREL CHOR / AFP
Talla

Masu zanga-zangar wadanda suka rufe fuskokinsu, a wannan karon sun samu damar kai wa ga ofishin jakadancin na China da ke Hong Kong, tare da fadin ba ma bukatar mulkinku.

Duk da dai gwamnatin Hong Kong tun tuni ta sanar da janye shirin fara aikewa da masu laifi don fuskantar hukunci a Beijin wanda ya haddasa boren, har yanzu matasan na ci gaba da boren ne don ganin gwamnatin ta janye duk wani yunkurin sanya kasar ta China a al’amuran tafiyar da mulki.

Tsawon makwanni 7 kenan al’ummar yankin ciki har da dalibai a matakai daban-daban na gudanar da zanga-zangar wadda it ace irinta ta farko da Hong Kong ta fuskanta a tarihi.

Bayan da suka kashe manyan titunan da ke sada jami’an tsaro da ofishin jakadancin Chinan, daya daga cikin masu zanga-zangar da ba a bayyana sunansa ba, bai kuma bude fuskarsa ba, ya karanto bukatunsu ta hanyar amfani da amsa kuwa.

Cikin kalamansa, mai gabatar da jawabin wanda bai gaza shekaru 19 ba, ya ce, za su kare yankinsu da al’ummarsu daga katsalandan din China, yana mai cewa Chinan na kokarin yi musu shisshigi a tsarinsu na shari’a da shugabanci, wanda ya zama dole ta janye a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.