Isa ga babban shafi
Afghanistan

Mataimakin shugaban Afghanistan ya tsallake rijiya da baya

Mataimakin shugaban kasar Afghanistan Abdul Rashid Dostum ya tsallake rijiya da baya, a wani farmaki da mayakan Taliban suka kaiwa jerin gwanon motocinsa, inda suka hallaka mai tsaron lafiyarsa daya.

Mataimakin shugaban kasar Afghanistan Abdul Rashid Dostum.
Mataimakin shugaban kasar Afghanistan Abdul Rashid Dostum. AFP/NOORULLAH SHIRZADA
Talla

Musayar wutar da aka shafi sa’a guda ana yi tsakanin masu tsaron lafiyar mataimakin shugaban, da kuma mayakan na Taliban, ta auku ne a arewacin Lardin Balkh, inda Dostum ya jagoranci wani gangamin siyasa.

Yayin jawabi a taron siyasar, Dostum yayi ikirarin zai iya shafe mayakan Taliban dake arewacin kasar ta Afghanistan daga Doron kasa cikin watanni 6, muddin gwamnati ta bashi dama.

A baya dai an sha kaiwa mataimakin shugaban na Afghanistan hari da nufin hallaka shi, ciki harda farmakin watan Yuli na shekarar bara da aka hallaka mutane 23 a birnin Kabul, wanda mayakan IS suka yi ikirarin kaiwa.

A baya dai kungiyoyin kare hakkin dan adam sun sha zargin AbdulRashid Dostum, daya daga cikin jagororin kabilar Uzbek, da aikata laifukan cin zarafin dan adam da suka hada da fyade da kuma azabtarwa, amma duk da haka a shekarar 2014, shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya zabe shi a matsayin mataimakinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.