Isa ga babban shafi
Yemen-Houthi

Sojin Yemen sun hallaka 'yan tawayen Houthi 73 cikin kwanaki 2

Rahotanni sun ce wani harin dakarun sojin Yemen a gabashin birnin Hodeida ya hallaka ‘yan tawayen Houthi 73 tsakanin jiya asabar da yau Lahadi, bayan gaza cimma matsaya a taron sasanta rikicin kasar da ya gudana a Geneva ranar Juma’a.

Rikicin dai ya biyo bayan gaza cimma matsaya a tattaunawar sulhun da aka shirya farawa kan rikicin na Yemen a birnin Geneve.
Rikicin dai ya biyo bayan gaza cimma matsaya a tattaunawar sulhun da aka shirya farawa kan rikicin na Yemen a birnin Geneve. REUTERS/Naif Rahma TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Tashar talabijin ta Al-Ekhbariya mallakin Saudiyya ta ce yayin sumamen karkashin jagorancin rundunar Amaliqa dakarun na Yemen sun kame tarin ‘yan tawayen ciki har da wasu jagororinsu baya ga kwace tarin makamai, ko dai an hallaka wasu soji 11 baya ga jikkata wasu 17.

Haka zalika majiyar ta ce sojin sun kuma taimaka wajen tseratar da tarin fararen hula da ke yanki yankin wanda ‘yan tawayen suka yiwa kawanya.

A juma'ar da ta gabata ne bangarorin biyu suka gaza cimma matsaya a tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ke shiga tsakani da ta gudana a birnin Geneva, ko da dai Yemen ta dora alhakin lalacewar tattaunawar kan 'Yan tawaye wadanda ta ce sun gaza halarta kamar yadda aka tsara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.